마태복음 18장 하우사어 신약
- 1 Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Wanene mafi girma a mulkin sama?''
- 2 Sai Yesu ya kira karamin yaro gunsa, ya sa shi a tsakaninsu,
- 3 ya ce, ''Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama.
- 4 Saboda haka, duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron nan, shi ne mafi girma a mulkin sama.
- 5 Duk wanda ya karbi karamin yaro a suna na, ya karbe ni.
- 6 Amma duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku.
- 7 Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo!
- 8 Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka.
- 9 Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu.
- 10 Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama.
- 11 [Dan Mutum ya zo ya ceci abinda ya bata].
- 12 Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba?
- 13 In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba.
- 14 Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka.
- 15 Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan.
- 16 Amma in ya ki ya saurare ka, ka je da 'yan'uwa biyu ko uku su zama shaidu, don ta wurin shaidu biyu ko uku ake tabbatar da kowacce kalma.
- 17 In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umme da mai karbar haraji.
- 18 Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama.
- 19 Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi.
- 20 Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su.''
- 21 Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''
- 22 Yesu ya amsa ya ce masa, ''Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in.
- 23 Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarki da yake so ya lisafta dukiyarsa dake a hannun barorinsa.
- 24 Da ya fara yin haka, sai aka kawo masa daya daga cikin barorinsa da yake binsa talanti dubu goma.
- 25 Amma tunda ba shi da abin biya, ubangidansa ya bada umurni a sayar da shi, tare da matarsa da 'ya'yansa da duk mallakarsa, domin a biya.
- 26 Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.”
- 27 Don haka ubangidansa yayi juyayi, sai ya ce, ya yafe bashin, a saki baran.
- 28 Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, 'Ka biya bashin da nake bin ka.'
- 29 Amma dan'uwansa bara ya roke shi ya ce, kayi mani hakuri, zan biya ka duk abinda na karba.'
- 30 Amma baran nan na farko ya ki. A maimakon haka, ya sa aka jefa dan'uwansa bara a kurkuku sai ya biya bashin nan.
- 31 Da sauran barori suka ga abin da ya faru, suka damu kwarai. Sai suka je suka fada wa ubangidansu yadda abin ya faru duka.
- 32 Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, ''Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni.
- 33 Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan'uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?'
- 34 Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa.
- 35 Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba.''