요한복음 2장 하우사어 신약
- 1 Bayan kwana uku, akwai aure a Kana ta Galili, mahaifiyar Yesu kuma tana wurin.
- 2 An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa auren.
- 3 Da ruwan inabin ya kare, maihafiyar Yasu tace masa, “basu da ruwan inabi.”
- 4 Yesu yace mata, “Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna”.
- 5 Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, “Ku yi duk abin da yace maku.”
- 6 To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda.
- 7 Yesu yace masu, “Cika randunan da ruwa”. Sai suka cika randunan makil.
- 8 Sai yace wa ma'aikatan, “Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki.” Sai suka yi hakannan.
- 9 Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango
- 10 yace masa, “Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu.”
- 11 Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi.
- 12 Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki.
- 13 To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima.
- 14 Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin.
- 15 Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu.
- 16 Yace wa masu sayar da tantabaru, “Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci.”
- 17 Almajiransa suka tuna a rubuce yake, “Himma domin gidanka za ta cinye ni.”
- 18 Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?”
- 19 Yesu ya amsa, “Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi.”
- 20 Sai shugabanin Yahudawa suka ce, “An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?”
- 21 Amma yana nufin haikali na jikinsa ne.
- 22 Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada.
- 23 Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi.
- 24 Amma Yesu bai yadda da su ba domin ya san su duka,
- 25 saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.