고린도전서 3장 하우사어 신약
- 1 Amma ni, yan'uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu.
- 2 Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba.
- 3 Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane?
- 4 Domin in wani ya ce, “Ina bayan Bulus,” wani kuma ya ce, “Ina bayan Afollos,” ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba?
- 5 To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka.
- 6 Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma.
- 7 Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman.
- 8 Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa.
- 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma.
- 10 Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin.
- 11 Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu.
- 12 Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka,
- 13 aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi.
- 14 Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada;
- 15 amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta.
- 16 Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku?
- 17 Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke.
- 18 Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama” wawa” domin ya zama mai hikima.
- 19 Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima a cin makircin su.”
- 20 Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.”
- 21 haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne,
- 22 Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne,
- 23 Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.