고린도전서 6장 하우사어 신약
- 1 Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi?
- 2 Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci?
- 3 Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai?
- 4 Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba?
- 5 Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa?
- 6 Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba!
- 7 Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba?
- 8 Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne!
- 9 Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu,
- 10 da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah.
- 11 Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
- 12 Dukkan abu halal ne a gare ni”, amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. “Dukan abu halal ne a gare ni,” amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba.
- 13 “Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne”, amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji.
- 14 Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa.
- 15 Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake!
- 16 Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan?
- 17 Kamar yadda Littafi ya fadi, “Su biyun za su zama nama daya.” Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan.
- 18 Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa.
- 19 Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne?
- 20 An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.