고린도후서 6장 하우사어 신약
- 1 haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah.
- 2 Domin ya ce, “A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku.” Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto.
- 3 Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani.
- 4 Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala,
- 5 duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa,
- 6 cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna.
- 7 Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu.
- 8 Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne.
- 9 Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba.
- 10 Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai.
- 11 Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke.
- 12 Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu.
- 13 Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku.
- 14 Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu?
- 15 Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya?
- 16 ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: ''Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.”
- 17 Sabili da haka, ''Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu,'' in ji Ubangiji. ''Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku.
- 18 Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni,'' in ji Ubangiji Mai iko duka.