갈라디아서 1장 하우사어 신약
- 1 Wannan Bulus manzo ne. Manzancina kuwa, bai zo daga mutane ba ko mutum, amma ta wurin Yesu Almasihu da Allah Uba wanda da ya tashe shi daga matattu.
- 2 Ni da dukan 'yan'uwa da nake tare da su a nan, ina rubuto maku ku iklisiyoyi da ke a Galatiya.
- 3 Alheri zuwa gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangjinmu Yesu Almasihu,
- 4 wanda ya ba da kansa domin zunubanmu saboda ya kubutar da mu daga wannan mugun zamani, bisa ga nufin Allah da Ubanmu.
- 5 Daukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin.
- 6 Na yi mamaki kwarai yadda kuka juya da sauri zuwa wata bishara daban. Na yi mamakin cewa kuna juyawa daga shi wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu.
- 7 Ba wata bishara, amma akwai wadansu mutane da suke kawo maku rudani kuma suna so su gurbata bisharar Almasihu.
- 8 Amma, ko da mu ne ko mala'ika daga sama ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda muka yi shelar ta, la'ananne ne.
- 9 Kamar yadda muka fadi maku a da, yanzu kuma ina sake fada, “Idan wani ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda kuka karba, la'ananne ne.”
- 10 To yanzu ina neman shaidar mutane ne ko Allah? Ina neman in gamshi mutane ne? Idan har yanzu ina kokarin in gamshi mutane ne, ni ba bawan Almasihu ba ne.
- 11 Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba.
- 12 Ban karbe ta daga mutum ba, ba ma wanda ya koyar mani A maimakon haka, ta wurin wahayin Yesu Almasihu ne zuwa gare ni.
- 13 Kun riga kun ji game da rayuwa ta a da cikin Yahudanci, yadda da nake da kwazon tsananta wa iklisiyar Allah fiye da misali kuma ina lalatar da ita.
- 14 Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina.
- 15 Amma ya gamshi Allah ya zabe ni daga cikin mahaifiyata. Ya kira ni ta wurin alherinsa.
- 16 Ya bayyana dansa a gareni, saboda in yi shelar sa cikin al'ummai. Nan da nan, ban nemi shawarar nama da jini ba
- 17 kuma ban tafi Urushalima ba wurin wadanda suka zama manzanni kafin ni. Maimakon haka sai na tafi Arebiya, daga nan sai na dawo Dimashku.
- 18 Bayan shekara uku na je Urushalima don in san Kefas, na zauna da shi na kwana goma sha biyar.
- 19 Amma ban ga ko daya daga cikin manzannin ba sai Yakubu kadai, dan'uwan Ubangiji.
- 20 Duba, a gaban Allah, ba karya nake yi ba cikin abin da na rubuta maku.
- 21 Daga nan sai na je lardin Suriya da Kilikiya.
- 22 Har a lokacin babu wanda ya san ni a fuska a iklisiyoyin Yahudiya da suke cikin Almasihu,
- 23 amma sai labari kawai suke ji, “Wanda a da yake tsananta mana yanzu yana shelar bangaskiyar da a da yake rusarwa.”
- 24 Suna ta daukaka Allah saboda ni.