에베소서 1장 하우사어 신약
- 1 Bulus, manzon Yesu Almasihu ta wurin nufin Allah, zuwa ga kebabbu na Allah da ke a Afisa wanda suke aminci cikin Yesu.
- 2 Bari alheri ya kasance da ku, da salama daga wurin Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
- 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine ya albarkace mu da kowanne albarku na ruhaniya da ke cikin sammai cikin Almasihu.
- 4 Kafin halitar duniya, Allah ya zabe mu da muka ba da gaskiya cikin Yesu. Ya zabe mu domin mu yi zaman tsarki da rayuwar da babu aibu a gabansa.
- 5 Cikin kauna Allah ya kaddara ya dauke mu mu zama yayansa ta wurin Yesu almasihu. Ya yi wannan domin ya gamshe shi ya yi abin da ya ke so.
- 6 Sakamakon shine Allah ya karbi yabo domin daukakan alherinsa. Wannan shine abinda ya ba mu hannu sake ta wurin kaunataccensa.
- 7 Gama cikin kaunataccensa aka fanshe mu ta wurin jininsa, da gafarar zunubai ta wurin wadataccen alherinsa.
- 8 Ya ba da wannan alherin a yalwace cikin dukan hikima da fahimta.
- 9 Allah ya bayyana mana gaskiyar al'amarin da aka boye na shirinsa, ta wurin abin da yake so ya nuna cikin Almasihu.
- 10 Idan lokaci ya yi na kammala shirinsa, Allah zai kawo dukan abubuwan da ke sama da kasa cikin Yesu.
- 11 An zabe mu cikin Almasihu mu zama abin gado na Allah. Ya yi mana wannan shirin tun da cikin shirin sa, shi mai yin dukan abu ta dalilin nufinsa.
- 12 Allah ya yi haka saboda mu rayu domin yabon daukakarsa. Mune na farko da muka sami bege cikin Almasihu.
- 13 A cikin Almasihu ne kuma kuka samu jin maganar gaskiya, bisharan cetonku ta wurin Yesu. A cikinsa ne kuka bada gaskiya aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.
- 14 Ruhun shine tabbacin gadonmu kafin mu kai ga samunsa. Wannan don yabon daukakarsa ne.
- 15 Sabo da haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kaunar ku zuwa dukan wadanda aka kebe dominsa.
- 16 Ban fasa tunawa da ku ba ina addu'a saboda ku cikin addu'o'ina.
- 17 Ina addu'a da cewa Allah Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban daraja, ya ba ku ruhun basira da wahayin saninsa.
- 18 Ina addu'a idanun zuciyarku su bude domin ku san tabacin kiranku. Ina addu'a dominku san arzikin mulkin gadonsa cikin wadanda aka kebe dominsa.
- 19 Ina addu'a ku san ikon nan nasa mai girma mara iyaka da ke cikin mu da muka ba da gaskiya. Wannan girman yana ta wurin aikin karfin ikonsa ne.
- 20 Wannan shine ikon da ya yi aiki cikin Almasihu lokacin da Allah ya tashe shi daga matattu ya sa shi a hannun damansa cikin sammai.
- 21 Ya sanya shi bisa birbishin dukan sarauta, iko, mulki, karfi, da kowanne irin suna. Ya sanya Almasihu ba a wannan zamanin kadai ba, amma da zamani mai zuwa.
- 22 Allah ya saka dukan abubuwa a karkashin kafafun Almasihu. Ya sa shi shugaban dukan abubuwa a cikin ikilisiya.
- 23 Ikilisiya jikinsa ne, cikarsa wanda ya cika dukan abubuwa cikin kowacce hanya.