에베소서 3장 하우사어 신약
- 1 Saboda haka, ni Bulus, dan sarka sabili da Almasihu dominku al'ummai.
- 2 Ina zaton kun ji a kan aiki mai girma na alherin Allah da ya ba ni dominku.
- 3 Ina rubuto maku bisa ga wahayin da aka sanashe ni. Wannan ita ce boyayyar gaskiya da na rubuta a takaice a cikin wata wasikar.
- 4 Sa'adda kuka karanta a kan wannan, za ku iya fahimtar basira ta cikin boyayyar gaskiya a kan Almasihu.
- 5 Wanda a zamanun da ba a bayyana wa mutane ba. Amma yanzu an bayyana shi ga manzanni da annabawa kebabbu a cikin Ruhu.
- 6 Wannan boyayyar bishara ita ce al'ummai ma abokan gado ne tare da mu, gabobi ne cikin jiki daya. Abokan tarayya ne kuma cikin alkawaran Almasihu Yesu ta wurin bishara.
- 7 Domin wannan na zama bawa ta wurin baiwar alherin Allah da ya bani ta wurin karfin ikonsa.
- 8 Allah ne ya ba ni wannan baiwa. Ko da shike nine mafi kankanta cikin kebabbun Allah, in yi shelar bishara ga al'ummai akan wadatar Almasihu marar matuka.
- 9 In kuma fahimtar da dukan mutane a kan shirin Allah, wannan boyayyar gaskiya wadda tun zamanai da suka wuce Allah ya boye, shi da ke mahallicin dukan abubuwa.
- 10 Saboda haka, ta wurin ikilisiya, masu iko da masu mulkin sararin sama za su san hikimar Allah ta fuskoki daban daban.
- 11 Wannan ya kasance bisa ga dawwamammen nufi da ya zartar cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
- 12 Gama a cikin Almasihu muna da gabagadi, da dama, da amincewa sabili da gaskiyar mu a cikinsa.
- 13 Saboda haka ina rokon ku kada ku karaya da wahalar da na sha domin ku wadda ta zama daukakar ku.
- 14 Saboda haka nake durkusawa da gwiwa ta a gaban Uba,
- 15 wanda ta wurinsa ake kiran kowanne iyali na sama da na kasa.
- 16 Ina addu'a ya amince maku bisa ga yalwar wadatar daukakarsa, ku karfafa matuka da iko ta wurin Ruhunsa, da yake cikinku.
- 17 Ina addu'a Almasihu ya zauna a cikin zuciyar ku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi kwarai cikin kaunarsa.
- 18 Ku kasance cikin kaunarsa domin ku gane, tare da dukan masu bi, menene zurfi, da fadi, da tsawon kaunar Almasihu.
- 19 Ina addu'a domin ku san mafificiyar kaunar Almasihu da ta wuce sani. Ku yi wannan domin a cika ku da dukan cikar Allah.
- 20 Yanzu ga wanda yake da ikon aikata dukan abu fiye da abin da muke roko ko tunani, bisa ga ikonsa da ke aiki a cikinmu,
- 21 daukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu har ya zuwa zamanun zamanai har abada abadin. Amin.