에베소서 5장 하우사어 신약
- 1 Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa.
- 2 Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah.
- 3 Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi.
- 4 Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya.
- 5 Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah.
- 6 Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya.
- 7 Kada ku yi tarayya tare da su.
- 8 Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske.
- 9 Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya.
- 10 Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi.
- 11 Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su.
- 12 Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su.
- 13 Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su.
- 14 Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, “Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka”.
- 15 Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima.
- 16 Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne.
- 17 Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji.
- 18 Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki.
- 19 Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji.
- 20 Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba.
- 21 Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu.
- 22 Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji.
- 23 Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki.
- 24 Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu.
- 25 Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta,
- 26 Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma.
- 27 Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi.
- 28 Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa.
- 29 Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya.
- 30 Domin mu gabobin jikinsa ne.
- 31 “Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya”.
- 32 Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa.
- 33 Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.