골로새서 3장 하우사어 신약
- 1 Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah.
- 2 Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba.
- 3 Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah.
- 4 Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa.
- 5 Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka.
- 6 Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya.
- 7 A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu.
- 8 Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku.
- 9 Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa,
- 10 kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi.
- 11 A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka.
- 12 A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri.
- 13 Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku.
- 14 Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla.
- 15 Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya.
- 16 Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah.
- 17 Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
- 18 Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji.
- 19 Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu.
- 20 Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai.
- 21 Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya.
- 22 Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji.
- 23 Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba.
- 24 Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa.
- 25 Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.