데살로니가후서 3장 하우사어 신약
- 1 Yanzu yan'uwa, ku yi mana addu'a saboda maganar Ubangiji tayi sauri ta sami daukaka, kamar yadda take tare da ku.
- 2 Ku yi addu'a domin mu kubuta daga mutane masu mugunta da keta, gama ba kowa ke da bangaskiya ba.
- 3 Amma Ubangiji mai aminci ne, shi wanda zai kafa ku ya tsare ku daga mugun.
- 4 Muna da gabagadi cikin Ubangiji a kan ku, cewa kuna yi, kuma za ku ci gaba da yin abubuwan da muka umurta.
- 5 Ubangiji ya bi da zuciyarku zuwa kaunar Allah da kuma jimrewar almasihu.
- 6 Yanzu muna umurtar ku, yan'uwa, a cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, ku guji duk dan'uwa wanda yake zaman banza ba kuma akan al'adun da kuka karba daga wurin mu ba.
- 7 Saboda ku da kan ku kun sani yana da kyau kuyi koyi da mu. Ba mu yi zama a cikin ku kamar wadanda ba su da tarbiya ba.
- 8 Ba mu kuma ci abincin kowa ba tare da mun biya ba. Maimakon haka, mun yi aiki dare da rana cikin wahala da kunci domin kada mu dora wa kowa nauyi.
- 9 Mun yi haka ba don ba mu da iko ba. Maimakon haka, mun yi wannan ne saboda mu zama abin koyi a wurin ku, domin ku yi koyi da mu.
- 10 Lokacin da muke tare da ku, mun umurce ku, “Duk wanda ba ya son yin aiki, kada yaci abinci.”
- 11 Saboda mun ji cewa wasun ku sun ki yin aiki. Ba su aiki sai dai shiga shirgin wasu.
- 12 Irin wadannan, muke umurta da kuma karfafa wa cikin Ubangiji Yesu Almasihu, da su yi aiki da natsuwa, suna cin abincin kan su.
- 13 Amma ku yan'uwa, kada ku rabu da yin abinda ke daidai.
- 14 In wani yaki biyayya da kalmominmu cikin wannan wasika, ku kula da shi kuma kada kuyi ma'amalar komai dashi, saboda ya ji kunya.
- 15 Kada ku dauke shi a matsayin makiyi, amma ku gargade shi a matsayin dan'uwa.
- 16 Bari Ubangijin salama da kansa ya ba ku salama kulluyaumin ta kowace hanya. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.
- 17 Wannan ita ce gaisuwa ta, ni Bulus, da hannuna, wanda shine alama a kowace wasika ta. Haka nake rubutu.
- 18 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku duka.