디모데전서 4장 하우사어 신약
- 1 To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu,
- 2 cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta.
- 3 Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar.
- 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba.
- 5 Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a.
- 6 Idan ka tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi.
- 7 Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah.
- 8 Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa.
- 9 Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum.
- 10 Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
- 11 Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa.
- 12 Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki.
- 13 Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa'azi, da kuma koyarwa.
- 14 Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa'ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu.
- 15 Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa.
- 16 Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.