디모데후서 3장 하우사어 신약
- 1 Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala.
- 2 Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki.
- 3 Za su kasance marasa dabi'a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, 'yan tawaye, marasa kaunar nagarta.
- 4 Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah.
- 5 Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen.
- 6 A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha'awoyi dabam daban.
- 7 Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba.
- 8 Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya.
- 9 Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane.
- 10 Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi'ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina,
- 11 da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni.
- 12 Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani.
- 13 Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire.
- 14 Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya.
- 15 Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu.
- 16 Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci.
- 17 Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.