히브리서 1장 하우사어 신약
- 1 A zamanin da, Allah ya yi wa kakanin kakanninmu magana ta hanyoyi ma su yawa iri iri, ta bakin annabawa.
- 2 Amma a zamanin nan na karshe, ya yi mana magana ta wurin Dansa, wanda ya sa magajin kome, wanda ta wurinsa ya halicci duniya.
- 3 Shi ne hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa. Ya na rike da dukkan abubuwa ta ikon kalmarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a hannun dama na madaukaki a can sama.
- 4 Ta haka ya ke da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gada yake da fifiko nesa a kan nasu.
- 5 Domin kuwa wanene a cikin mala'iku Allah ya taba cewa, “Kai Da na ne, yau na zama Uba a gare ka?'' kuma, “Zan kasance Uba a gareshi, shi kuma, zai kasance Da a gare ni?''
- 6 Kuma, da Allah ya kawo magaji a duniya, sai ya ce, “Dukan mala'ikun Allah su yi masa sujada.”
- 7 A game da mala'iku kuma sai ya ce, “yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta.
- 8 A game da Dan, ya ce “kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne. Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya.
- 9 Ka kaunaci aikin adalci, ka ki aikin sabo. Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka da man farin ciki fiye da tsararrakinka.”
- 10 “Tun farko, Ubangiji, kai ne ka hallici duniya. Sammai kuma aikin hannayenka ne.
- 11 Za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufafi.
- 12 Za ka nade su kamar mayafi, za su kuma sauya, amma kai kana nan ba sakewa, Har abada shekarunka ba za su kare ba.”
- 13 Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taba cewa, “Zauna a hannun dama na, sai na sa makiyanka a karkashin kafafunka?''
- 14 Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi, wadanda Allah yakan aika, don su yi wa wadanda za su gaji ceto hidima?