히브리서 3장 하우사어 신약
- 1 Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la'akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu.
- 2 Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah.
- 3 Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka.
- 4 Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah.
- 5 Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba.
- 6 Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu.
- 7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: ''Yau, Idan kun ji muryarsa,
- 8 kada ku taurare zuciyarku kamar yadda 'ya'yan isra'ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji.
- 9 A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba'in suna ganin ayyukana.
- 10 Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,' Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.'
- 11 Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba.”
- 12 Ku yi hankali 'yan'uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai.
- 13 Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi.
- 14 Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe.
- 15 Game da wannan, an fadi “Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan.”
- 16 Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne?
- 17 Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba'in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji?
- 18 Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba?
- 19 Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.