히브리서 8장 하우사어 신약
- 1 Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai.
- 2 Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba.
- 3 Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya.
- 4 Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan.
- 5 Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: ''Duba'' Allah ya ce, ''kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse.”
- 6 Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura.
- 7 Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu.
- 8 Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce ''Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza.
- 9 kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su,'' inji Ubangiji.
- 10 Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata.
- 11 Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, ''ku san Ubangiji'' gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba.
- 12 Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba.
- 13 A kan fadin ''sabo'' ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.