베드로전서 2장 하우사어 신약
- 1 Saboda haka sai ku tube dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance.
- 2 Kammar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai ruhaniya wadda take sahihiya, domin ta wurinta kuyi girma zuwa ceto,
- 3 idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne.
- 4 Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah.
- 5 Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu.
- 6 Gama nassi ya ce, “Ga shi na sanya dutse na kan kusurwa, zababe, mai daraja a cikin Sihiyona. Duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zaya kunyata ba.”
- 7 Daraja a gareku take ku da kun bada gaskiya. Amma, ga wadanda suka ki bada gaskiya, “Dutsen da magina suka ki shine aka mai she shi kan kusurwa”.
- 8 kuma, “Dutsen sa tuntube da fa na sa tuntube. “Sun yi tuntube, da shike sun ki biyayya da maganar, an kuwa kaddara su ga wannan.
- 9 Amma ku zababben jinsi ne, kungiyar fristoci ba-sarauci, al'umma mai-tsarki, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wanda ya kiraye ku daga chikin duhu zuwa cikin haskensa mai'ban al'ajibi.
- 10 Ku da ba jama'a ba ne a da, amma yanzu jama'ar Allah ne. Da baku sami jinkai ba, amma yanzu kun sami jinkai.
- 11 Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai.
- 12 Ku kasance da kyakkyawan hali a cikin al'ummai, domin, sa'adda suke kushen ku kamar masu aikata mugunta, sai su lura da nagargarun ayyukanku su kuma daukaka Allah a ranar zuwansa.
- 13 Kuyi biyayya ga kowacce hukuma ta mutane sabili da Ubangiji, ko ga sarki domin shi ne shugaba.
- 14 Ko kuwa ga masu mulki aikakkunsa ne domin su hori masu aikata mugunta da yabawa masu aikata nagarta.
- 15 Gama wannan nufin Allah ne, ta wurin aikin kirki ku, kwabi jahilcin mutane marassa hikima.
- 16 Kamar 'yan'tattu kada ku mori 'yan'cinku kamar mayafin mugunta, amma ku zama kamar bayin Allah.
- 17 Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki.
- 18 Ku barori, kuyi biyayya ga iyayen gidanku da dukkan bangirma, ba ga nagargaru da masu saukin kai ba, amma har ga miskilai.
- 19 Gama abin yaba wa ne idan sabili da lamiri zuwa ga Allah in wani ya jimre da shan zalunci.
- 20 Gama wacce riba ke nan idan kun yi zunubi ana horonku kuna jimrewa da hukuncin? amma idan kunyi aikin kirki kuka sha wuya a kansa kuka yi hakuri, wannan abin karba ne wurin Allah.
- 21 Gama akan haka aka kiraye ku, gama Almasihu ma yasha azaba saboda ku, ya bar maku gurbi kubi sawunsa.
- 22 Bai taba yin zunubi ba, ba'a taba jin yaudara a bakinsa ba.
- 23 Da'a ka zage shi bai mai da zagi ba. Da ya sha azaba, bai yi kashedi ba, amma ya mika kansa ga wanda yake yin shari'ar adalci.
- 24 Shi da kansa ya dauki zunubanmu a cikin jiki nasa ya kai su bisa itace, domin kada a iske mu cikin zunubi, amma muyi rayuwa ga adalci. Ta wurin raunukansa ne kuka warke.
- 25 Dukkanku da kun bata kuna yawo kamar batattun tumaki, amma yanzu kun dawo wurin makiyayi da mai tsaron rayukanku.