베드로전서 4장 하우사어 신약
- 1 Saboda haka, tunda yake Almasihu ya sha wuya a jiki, muma mu sha damara da wannan ra'ayi. Duk wanda ya sha wuya a jiki ya daina aikata zunubi.
- 2 Wannan mutum kuma baya kara zaman biye wa muguwar sha'awar mutumtaka, amma sai dai nufin Allah dukkan sauran kwanakinsa a duniya.
- 3 Gama lokaci ya wuce da zamu yi abin da al'ummai suke son yi, wato fajirci, mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama.
- 4 Suna tunanin bakon abu ku ke yi da ba kwa hada kai tare da su yanzu a yin wadannan abubuwa, sai suna zarginku.
- 5 Za su bada lissafi ga wanda yake a shirye ya shari'anta masu rai da matattu.
- 6 Shi yasa aka yi wa matattu wa'azin bishara, cewa ko da shike anyi masu shari'a cikin jikunan mutane, su rayu bisa ga Allah a ruhu.
- 7 Karshen dukkan abubuwa yana gabatowa. Saboda haka, ku zama natsatsu, ku natsu cikin tunaninku domin yin addu'oi.
- 8 Gaba da kome, ku himmatu wajen kaunar juna, domin kauna bata neman tona zunuban wadansu.
- 9 Ku yi wa juna bakunta da abubuwa nagari ba tare da gunaguni ba.
- 10 Yadda kowanne dayanku ya sami baiwa, kuyi amfani da su domin ku kyautata wa juna, kamar masu rikon amanar bayebaye na Allah, wanda ya ba mu hannu sake.
- 11 Idan wani yana yin wa'azi, ya zamana fadar Allah ya ke fadi, idan wani yana hidima, ya yi da karfin da Allah ya ba shi, domin cikin dukkan abubuwa a daukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Daukaka da iko nasa ne har abada abadin. Amin.
- 12 Ya kaunatattu, kada ku zaci cewa matsananciyar wahalar da ta zo ta gwada ku bakon abu ne, ko kuma wani bakon abu ne yake faruwa a gareku.
- 13 Amma muddin kuna tarayya da Almasihu cikin wahalarsa, ku yi murna, domin kuyi farin ciki da murna sa'adda za a bayyana daukakarsa.
- 14 Idan ana zargin ku sabili da sunan Almasihu, ku masu albarka ne, domin Ruhun daukaka da Ruhun Allah ya tabbata a kanku.
- 15 Amma kada kowannen ku ya sha wahala sabo da horon shi mai kisan kai ne, ko barawo, ko mamugunci, ko mai shisshigi.
- 16 Amma in wani yana shan wahala sabili da shi na Almasihu ne, kada ya ji kunya, amma ya daukaka Allah a wannan sunan.
- 17 Domin lokaci ya yi da shari'a za ta fara daga gidan iyalin Allah. Idan kuwa za a fara da mu, menene karshen wadanda suka ki biyayya da bisharar Allah?
- 18 Idan mutum, “mai adalci ya tsira da kyar, to, me zai faru da marar bin Allah da mai zunubi kuma?”
- 19 Sabo da haka bari wadanda suke shan wuya bisa ga nufin Allah, su mika rayukansu ga amintaccen Mahalicci suna kuma yin ayyuka nagari.