요한일서 4장 하우사어 신약
- 1 Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya.
- 2 Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne,
- 3 kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya.
- 4 'Ya'yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma.
- 5 Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu.
- 6 Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya.
- 7 Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah.
- 8 Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne.
- 9 A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa.
- 10 A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu.
- 11 Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu.
- 12 Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu.
- 13 Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa.
- 14 Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya.
- 15 Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
- 16 Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa.
- 17 Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari'a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan.
- 18 Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna.
- 19 Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu.
- 20 Idan wani ya ce,”Ina kaunar Allah”, amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba.
- 21 Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan'uwansa.