고린도전서 15장 하우사어 신약
- 1 Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita.
- 2 Da wannan bishara aka yi maku ceto, idan kuka rike wa'azi da na yi maku da karfi, sai in dama kun gaskanta a banza.
- 3 Domin na baku muhimmin sako kamar na farko da na karba: cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi,
- 4 cewa kuma an bizne shi, ya kuwa tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi.
- 5 Cewa kuma ya bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun.
- 6 Daga nan ya bayyana ga 'yan'uwa sama da dari biyar a lokaci guda. Wadanda mafi yawan su na da rai har yau, amma wasun su sun yi barci.
- 7 Daga nan ya bayyana ga Yakubu, da kuma ga manzannin duka.
- 8 A karshe, sai ya bayyana a gare ni, kamar dan da aka haifa bakwaini.
- 9 Gama ni ne mafi kankanta a cikin manzanni. Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsanantawa ikklisiyar Allah.
- 10 Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni.
- 11 Saboda haka ko nine ko Su, haka mukayi wa'azin, haka kuma kuka gaskata.
- 12 To idan anyi shela a matsayin cewa Yesu ya tashi daga matattu, tayaya wadansunku su ke cewa babu tashin matattu?
- 13 Amma idan babu tashin matattu, Almasihu ma ai ba a tashe shi ba kenan.
- 14 idan kuwa ba a tashi Almasihu ba, wa'azin mu ya zama banza kenan, haka kuma bangaskiyar ku ta zama banza.
- 15 Mun kuma zama shaidun karya game Allah kenan, muna shaida akan Allah cewa ya tashi Almasihu daga matattu alhali ko bai tashe shi ba.
- 16 Domin idan babu tashin matattu, kai, ko Almasihu ma ba a tashe shi ba kenan.
- 17 Idan har ba a tashi Almasihu ba, bangaskiyar ku a banza take, har yanzu kuma, kuna cikin zunuban ku.
- 18 To wadanda suka mutu cikin Almasihu kuma sun hallaka kenan,
- 19 idan a wannan rayuwa ce kadai muke da bege cikin Almasihu, to cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi.
- 20 Amma yanzu, Almasihu ya tashi daga matattu, wanda ya sa shi ya zama nunar fari cikin tashi daga matattu.
- 21 Domin yadda mutuwa ta shigo duniya ta hanyar mutum guda, hakkan nan ma tashi daga matattu.
- 22 Gama kamar yadda a cikin Adamu duka suka mutu, haka kuma a cikin Almasihu za a rayar da duka.
- 23 Amma kowanne da tsarinsa: Almasihu, nunan fari, sannan su wadanda ke na Almasihu za a rayar da su lokacin zuwansa.
- 24 Sa'an nan karshen zai gabato, lokacin da Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba. sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko.
- 25 Gama mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a karkashin sawayen sa.
- 26 Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka.
- 27 Domin “ yasa dukkan komai a karkashin ikonsa,” Amma da aka ce” yasa dukkan komai a karkashin ikonsa,” a sarari yake cewa wannan baya hada da wanda yasa dukan komai a karkashin ikonsa ba.
- 28 Idan dukan abu na karkashin mulkinsa, to Dan da kansa zaya kasance a karkashin ikon shi wanda yasa komai a karkashin ikonsa. Wannan zaya kasance ne saboda Allah Uba ya zama dukkan komai cikin dukkan komai.
- 29 ko kuma me zai faru da wadanda ake yi wa baftisma domin matattu? Idan kuwa babu tashin matattu sam sam, ina amfanin yi masu baftisma domin su?
- 30 Kuma me yasa muke cikin hadari kowace sa'a?
- 31 Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
- 32 Menene ribata, a idanun mutane, idan nayi kokowa da bisashe a Afisa, idan babu tashin matattu? “ bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu.”
- 33 Kada fa a yaudare ku, domin “ tarayya da mugaye takan bata halayen kirki.”
- 34 “Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya.
- 35 Amma wani zaya ce, “Yaya za'a yi tashin matattu? Wane irin jiki kuma zasu tashi da shi?
- 36 Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu.
- 37 Abinda ka shuka ba jikin da zaya kasance bane, amma kwayar irin ne kawai. Wanda zaya zama alkama ko wani abu daban.
- 38 Amma Allah zaya bashi jiki yadda ya zaba, ga kowane kwayar iri da nashi jikin.
- 39 Ba duka jiki ne yake iri daya ba. A maimako, akwai jiki irin na mutane, akwai kuma wani irin na dabbobi, kuma wani jikin irin na tsuntsaye, kuma da irin na kifi.
- 40 Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya. Amma daukakar jikin samaniya wata daban ce kuma daukakar jikin duniya daban ce.
- 41 Akwai daukaka irin ta rana, da kuma wata daukakar irin ta wata, da kuma wata daukakar irin ta taurari. Domin wani tauraron ya bambanta da wani wajen daukaka.
- 42 Haka yake a tashin matattu. Abinda aka shuka mai lalacewa ne, wanda aka tayar marar lalacewa ne.
- 43 An shuka shi cikin rashin daraja; an tayar da shi cikin daukaka. An shuka shi cikin rauni; an tayar da shi cikin iko.
- 44 An shuka shi jiki na zahiri; an tayar da shi jiki na ruhaniya. Idan akwai jiki na zahiri, to akwai jiki na ruhaniya.
- 45 Haka kuma aka rubuta, “ Adamu na farko ya zama rayayyen taliki.” Adamu na karshe ya zama Ruhu mai bayar da rai.
- 46 Amma na ruhaniyar ba shine ya fara zuwa ba amma na zahirin, daga nan na ruhaniyar.
- 47 Mutumin farkon ai daga turbaya ya fito, wato na duniya. Amma shi na biyun daga sama yake.
- 48 kamar yadda mutumin ya fito daga turbaya haka ma wadanda aka halitta da turbaya. kamar yadda mutumin yake daga sama haka ma wadanda ke na sama.
- 49 Kamar yadda muke dauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama.
- 50 To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba.
- 51 Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu.
- 52 Za a canza mu nan da nan, cikin keftawar ido, a kaho na karshe. Domin za a busa kaho, kuma za a tada matattu marasa lalacewa, kuma za a canza mu.
- 53 Domin wannan jiki mai lalacewa dole ya sanya jiki marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa dole ya sanya marar mutuwa.
- 54 Amma idan wannan jiki mai lalacewa ya sanya marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa ya sanya marar mutuwa, sai abinda aka rubuta ya cika, “An hadiye mutuwa cikin nasara.”
- 55 “Mutuwa, ina nasararki? Mutuwa, ina dafinki?”
- 56 Gama dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce.
- 57 Amma godiya ga Allah, wanda ya bamu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu!
- 58 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana kaunatattu, ku dage kuma kada ku jijjigu. Ko yaushe ku habaka da aikin Ubangiji, domin kun san cewa aikinku cikin Ubangiji ba a banza yake ba.