고린도전서 16장 하우사어 신약
- 1 Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi.
- 2 A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba.
- 3 Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima.
- 4 Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni.
- 5 Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya.
- 6 Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni.
- 7 Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda.
- 8 Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos.
- 9 Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa.
- 10 Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
- 11 Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa.
- 12 Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi.
- 13 Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali.
- 14 Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna.
- 15 Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa,
- 16 kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu.
- 17 Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku.
- 18 Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane.
- 19 Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji.
- 20 Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki.
- 21 Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna.
- 22 Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo!
- 23 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku.
- 24 Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. [ Amin ].