골로새서 2장 하우사어 신약
- 1 Ina so ku san yadda na sha faman gaske dominku, domin wadanda ke a Lawudikiya, da kuma wadansu da yawa da a jiki basu taba ganin fuska ta ba.
- 2 Na yi aiki saboda zuciyar su ta sami karfafawa ta wurin hada su cikin kauna zuwa dukan arziki na tabbaci da fahimtar asirin gaskiya na Allah, wato Almasihu.
- 3 A cikinsa dukan taskar hikima da sani ke boye.
- 4 Na fadi haka domin kada wani ya yaudare ku da jawabi mai jan hankali.
- 5 Ko da yake ba na tare da ku a jiki, duk da haka ina tare da ku a cikin Ruhu. Ina murnar ganin ku a yanayi mai kyau da kuma karfin bangaskiyar ku cikin Almasihu.
- 6 Kamar yadda kuka karbi Almasihu Ubangiji, ku yi tafiya cikinsa.
- 7 Ku kafu da karfi a cikinsa, ku ginu a kansa, ku kafu cikin bangaskiya kamar yadda aka koya maku, ku yawaita cikin yin godiya.
- 8 Ku lura kada wani ya rinjaye ku ta hanyar ilimi da yaudarar wofi bisa ga al'adun mutane, bisa ga bin abubuwan duniya, ba na Almasihu ba.
- 9 A cikinsa ne dukan Allahntaka ta bayyana ta jiki.
- 10 Ku kuwa kun cika a cikinsa. Shine gaban kowanne iko da sarauta.
- 11 A cikinsa ne aka yi maku kaciya, ba kaciya irin da yan adam suke yi ba, ta cire fatar jiki, amma ta kaciyar Almasihu.
- 12 An binne ku tare da shi ta wurin baftisma. Kuma a cikinsa ne aka ta da ku ta bangaskiya a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga mutattu.
- 13 A lokacin da kuke matattu cikin laifofinku, a cikin rashin kaciyar ku ta jiki, ya rayar da ku tare da shi kuma ya yafe maku dukan laifofinku.
- 14 Ya share rubutattun basussukanku da ka'idodin da suke gaba da mu. Ya cire su duka ya kafa su a kan giciye.
- 15 Ya cire ikoki da sarautu. A fili ya falasa su ya shugabance su zuwa ga bukin nasara ta wurin giciyensa.
- 16 Saboda haka, kada kowa ya shari'anta ku ta wurin ci ko sha, ko kuma sabon wata, ko game da ranakun Assabaci.
- 17 Wadannan sune inuwar abubuwan da ke zuwa nan gaba, amma ainihin shi ne Almasihu.
- 18 Kada kowa wanda ke son kaskanci da sujadar mala'iku ya sharantaku ku rasa sakamakonku. Irin wannan mutum yana shiga cikin abubuwan da ya gani ya zama mai girman kai a tunaninsa na jiki.
- 19 Ba ya hade da kai. Daga kan ne dukan jiki da gabobi da jijiyoyi ke amfani suna kuma hade tare; yana girma da girman da Allah yake bayarwa.
- 20 In kun mutu tare da Almasihu ga ala'muran duniya, don me kuke rayuwa kamar kuna karkashin duniya:
- 21 “Kada ku rike, ko ku dandana ko ku taba?”
- 22 Dukan wadannan abubuwa karshen su lalacewa ne in ana amfani da su, bisa ga kaidodi da koyarwar mutane.
- 23 Wadannan dokoki suna da hikima ta jiki irin ta addini da aka kago na kaskanci da kuma wahalar da jiki. Amma ba su da amfanin komai a kan abin da jiki ke so.