골로새서 4장 하우사어 신약
- 1 Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama.
- 2 Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a. Ku zauna a fadake cikin addu'a da godiya.
- 3 Ku yi addu'a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka.
- 4 Ku yi addu'a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada.
- 5 Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci.
- 6 Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum.
- 7 Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan'uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji.
- 8 Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku.
- 9 Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan'uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan.
- 10 Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan'uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi),
- 11 da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta'aziya a gare ni.
- 12 Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu'a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah.
- 13 Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis.
- 14 Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku.
- 15 Ku gai da 'yan'uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta.
- 16 Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya.
- 17 Ku gaya wa Arkibas, “Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi.”
- 18 Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.