에베소서 4장 하우사어 신약
- 1 Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku.
- 2 Ku zamna da matukar tawali'u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna.
- 3 Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama.
- 4 Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya.
- 5 Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya.
- 6 Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka.
- 7 Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu.
- 8 Kamar yadda nassi ya ce, “Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye.
- 9 Menene ma'anar, “Ya hau?” Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa.
- 10 Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa.
- 11 Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa.
- 12 Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu.
- 13 Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu.
- 14 Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya.
- 15 Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu.
- 16 Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna.
- 17 Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al'ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani.
- 18 Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu.
- 19 Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari.
- 20 Amma ba haka kuka koyi al'amuran Almasihu ba.
- 21 Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke.
- 22 Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri.
- 23 Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku.
- 24 Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya.
- 25 Saboda haka ku watsar da karya. “Fadi gaskiya ga makwabcin ka”, domin mu gabobin juna ne.
- 26 “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi.” Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi.
- 27 Kada ku ba shaidan wata kofa.
- 28 Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu.
- 29 Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji.
- 30 Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa.
- 31 Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta.
- 32 Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.